Gizo yayi amarya

GIZO YAYI AMARYA

Gata nan gata nan ku...

Gizo ne dai suna zaman lafiyar su shi da koki garin kalle kallen shi ya gano 'yar gidan tururuwa.

Gizo ya debo wa kanshi yace ai shi yana sonta zai kuma aureta! su Gizo har da sakin koki!

Aka daura auren Gizo, su kuma su tururuwai aka sha biki aka gama aka kai amarya gidan Gizo. Da farko kamar abun arziki ana zaman lafiya komai Gizo yake so ana yi masa.

Bayan watanni haka ai tsiya ta fara...tururuwa ta daina yiwa Gizo abunda yake so! Ana haka sai rannan Gizo ya hadu da koki a hanya

koki: ashe Gizo an yame (rame), ashe Gizo an yame?

Gizo: in bayi (bari) dai koki! nayi karambani da na auyo (auro) 'yar gidan tururuwai. Baki na ta maujeje, baki na ta kwalele, cikin ta kamar kwarya, kafan ta kamar tsinke

Koki tace kai ka gano (sabidda ita koki tayi kyau babu abunda ya dameta) Shi kuwa Gizo wahala ta ramar dashi.

Nan dai Gizo ya tsaya wai shi dai gaskiya koki ta dawo - ya gaji da tururuwa - Koki sai da ta wahalar dashi sannan ta dawo! ita kuma 'yar tururuwa ya sake ta.

Gizo da koki suka koma kamar da tare da 'ya 'yansu. Gizo yayi kyau.

Kurunkus kan dan bera da ba dan gizo ba dana yi karya...

Ga bera nan Ga bera nan! Wanda yaji tsoro ba...

Post a Comment

0 Comments