Za'a yanke network din 3G: wato 3G zai dai na amfani a waya.
Manyan kanfaninnikan guda Uku dasu ke watsa 3G ga wayoyin hannu dan shiga yanar gizo da suke Amurka sun saka ranar kulle 3G network acikin shekaran 2022.
Wa innan kanfanonin sune AT&T, T-Mobile, or Verizon, kuma indai ka/ki na amfani dasu to zai shafi wayan ka/ki. Aguguwan dazai shafa bai tsaya ga waya ba kawai harda duk wani na'ura mai anfani da 3G killa mota, modem, da sauran su duk suma zasu tsaya.
Amma ga bayanin dalla dalla.
AT&T zata fara daukewa daga 22 February, 2022.
Sprint 3G da sunce July 1, 2022 amma yanzu sun daga zuwa May 31, 2022.
3G kuma na T-Mobile zai daina aiki July 1, 2022 amma 2G din su zai ci gaba amma shima akan wani tsari.
Verizon kuma sai December 31, 2022
Sunce amman za su tuntube mutum in kullewan ya shafi mutum kuma kila suba ka kyautan waya mai 4G ko 5G.
Iphone kuma wacce kamfanin Apple ke kera wa sunce Iphone 6 zuwa sama baza su sami matsalan ba akan komi amma wasu wayoyin kamar wasu samsung da network din su bana US bane za'a cire su daga network din musamman na network din wayoyin AT&T. Wato kenan daga iphone 5 kasa suma abun zai shafe su.
MEYASA ZA'A KULLE NETWORK DIN?
Da farko dai 3G sun tsufa sabidda 3G dai an dan kara bude 2G ne shiyasa aka same shi tun fasahan 1995-1996. T-mobile sun samar da 3G tun 2006-2007 ne. Yanzu dai sunce 3G yana sa su kashe kudi sosai me yawa, bayan 5G yana aikin 3G ninki 23 wato zai iya daukan masu amfani da network din har 23 sabida sabuwan fasaha.
Sabida haka ana bada shawara a gaya wa wa'inda suke amfani da 3G android ko iphone su canza kafin ya shafe su.
Kuma wata Majiya tace August mai zuwa zasu dai na aika a duniya baki daya.
0 Comments